Isa ga babban shafi
Najeriya

An kai wa mabiya Shi’a harin bom a Potiskum

Akalla mutane 15 suka mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai wa mabiya Shi’a a garin Potiskum Jihar yobe a Najeriya. harin kuma ya jikkata mutane sama da 50, kamar yadda wani shugabannin mabiya Shi’a a yankin ya tabbatar. Malamin yace an kai wa mabiyansu hari ne a yayin da suke gudanar da bikin Ashura a garin Potiskum.

Jami'an tsaron Najeriya
Jami'an tsaron Najeriya Reuters
Talla

Kuma yace an samu mutuwar mutane 15 ne bayan da Sojoji suka bude wuta da zuwansu inda aka kai harin. Zuwa yanzu babu wani bayani daga Sojojin na Najeriya game da faruwar al’amarin.

Wani shedun gani da ido da wakilin RFI a Yobe ya zanta da shi  yace Maharin ya shiga cikin jerin mabiya Shi'a ne a lokacin da suke Mazahara kafin ya dalawa kansa Bom. nan take ne kuma aka samu gawawwakin mutane zube a kasa.

01:17

Rahoto: An kai wa mabiya Shi’a harin bom a Potiskum

RFI

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.