Isa ga babban shafi
Nijar

Hama Amadou ya gudu zuwa Burkina Faso

Rahotanni daga Nijar sun ce Shugaban Majalisar Dokokin kasar Hama Amadou ya tsere zuwa kasar Burkina Faso domin gujewa bincike akan zargin da ake masa na sayen Jarirai da aka yo ma sa fataucinsu daga Najeriya.

Shugaban Majalisar Dokokin Nijar  Hama Amadou.
Shugaban Majalisar Dokokin Nijar Hama Amadou. AFP PHOTO STEPHANE DE SAKUTIN
Talla

Tuni Kwamitin gudanarwar Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ya amince da bukatar da gwamnatin kasar ta gabatar na gurfanar da shugaban Majalisa Hamma Amadou a gaban kotu kan cinikin jirajirai.

Ana zargin shugaban Majalisar dokokin ne da sayen Jarirai da aka yo fataucinsu daga Najeriya zuwa Nijar.

Tun a watan Yuni aka cafke Matar Hama Amadou da wasu mutane 17 da ciki har da Mata 12 da ake zargi sun sayo Jarirai.

Amma tuni Hama Amadou ya karyata zargin wanda ake gani babban dan siyasar da zai kalubalanci Mahamadou Issoufou a zaben shugaban kasa a 2016. Hama ya danganta al’amarin da yarfe na siyasa da yunkurin cire masa rigar kariya

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Mohammed Ben Omar ya shaidawa RFI Hausa cewa dole sai Hama Amadou ya mika kansa domin fuskantar Shari’a.

Sai dai bangaren marasa rinjaye sun yi korafi kan matakin inda suka bukaci bin dokar kasa.

Akwai yiyuwar Hama Amadou zai kalubalanci matakan da aka dauka akansa a kotun kundin tsarin mulki.

Tun a ranar Assabar ne dai aka cafke Ministan Noma Abdou Labo wanda ake zargi da hannu a cikin badakalar cinikin Jariran.

Masu sharhi dai suna ganin Matan ‘Yan siyasar ne suka tursasa ma su sayen Jariran saboda matsalar rashin haihuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.