Isa ga babban shafi
Nigeria

Ebola: an hana kai gawarwakin 'yan Najeriya da suka mutu a kasashen waje zuwa kasar

Bayan da wani dan kasar liberiya ya mutu sakamakon cutar Ebola a Nigeria, Gwamnatin kasar ta hana kai gawarwakin ‘yan wadanda mutu a kasashe ketare, musamman inda cutar ta bulla, zuwa Nigeria. Hukumomin sun dauki wannan matakin ne don kaucewa bazuwar Ebola, bayan da kwararru suka tabbatar ana iya kamuwa da ita, in aka yi mu’amala da gawar wanda ya mutu sakamakon cutar.Babban daraktan cibiyar kiyaye yaduwar cututuka ta kasar, Farfesa Abdulsalami Nasidi yace ana bincike gawar wani dan Nigeria da aka kai daga Liberia, don tantace ko ya mutu ne sakamakon cutar ta Ebola.Ana ta cecekuce kan gawar mutumin dan asalin jihar Anambra da ya mutu a kasar Liberia, aka kuma kai shi kasar ta filin jirgin saman Murtala Muhammed dake birnin Lagos, a ranar 21 ga watan Yuli, da wasu ke zargin ya mutu ne sakamon cutra ta Ebola.An ajiye gawar mutumin ne a wani asibintin da ke jihar ta Anambra, kuma Farfesa Nasidi yace an tura wata tawaggar kwararru, da suka hada da wadanda suka zo daga hukumar lafiya ta duniya WHO, don sun gudanar da bincike kan lamarin.Ya kara da cewa, an nemo bayanai kan duk wadanda suka yi mu’amala da gawar mutumin, kuma yanzu haka ana nemansu don gudanar da bincike kan lafiyarsu. 

Hoton kwayar Cutar Ebola
Hoton kwayar Cutar Ebola CDC/ Cynthia Goldsmith
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.