Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana bikin Sallah a Najeriya

Al’ummar Musulmi a Najeriya a yau Lahadi ne suke gudanar da bikin sallah da ake kira Sallah karama bayan kammala Azumin watan Ramadan. Musulmi a Najeriya sun ajiye azumi ne bayan Mai alfarma Sakin Musulmi  Sa'ad Abubakar na uku  ya tabbatar da ganin watan Shawwal a wasu sassan Jihohin kasar.

Jami'an tsaro suna tantance masu shiga Masallacin Idi a birin Abuja
Jami'an tsaro suna tantance masu shiga Masallacin Idi a birin Abuja informationng.com
Talla

A sakonsa na Sallah ga Al’ummar musulmi, Shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana fatar samun zaman lafiya a Najeriya, tare da kira ga Musulmi su yi amfani da darussan da suka koya a Azumin Ramadana.

Shugaban kuma ya tabbatarwa al’ummar Najeriya cewa zasu kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi kasar tare da yin al’kawarin inganta rayuwar al’ummar Najeriya.

Kungiyar Jama’atul Nasril ta taya al’ummar Najeriya murnar kammala Azumin Ramadan, tare da kira ga Musulmi su yi amfani da darrussan da suka koya na Azumi ga harakokin rayuwarsu.

Bikin sallah a Najeriya na zuwa ne a daidai lokacin da Mayakan Boko Haram suka yi wa Mutane 12 yankar rago a yankin Biu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.