Mutane 21 suka mutu a harin Abuja
Akalla mutane 21 aka ruwaito sun mutu a wani harin bom da aka kai a wata cibiyar hada hadar kasuwanci a birnin Abuja, al’amarin da ya jikkata mutane kimanin 17. An kai harin ne a shagunan Emab Plaza a dai dai lokacin da Najeriya ke shirin fafatawa da Argentina a gasar cin kofin duniya a kasar Brazil.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kakakin ‘Yan sanda Frank Mba yace zuwa yanzu mutane 21 suka tabbatar da mutuwarsu, 17 suka jikkata. Akwai wani da ‘Yan sanda suka cafke wanda ake zargin yana cikin wadanda suka kai harin tare da bindige dan uwansa.
Emab Plaza, da ke yankin Wuse 11 wuri ne da ke hada cunkoson Jam’a kusa da Masallacin Juma’a kuma rahotanni sun ce kimanin motoci 40 ne suka kone.
Cikin wadanda suka mutu akwai Malam Suleiman Bisallah tsohon mataimakin editan Jaridar Daily Trust da ke aiki da sabuwar Jaridar New Telegraph.
Rahoton Aminu Manu daga Abuja
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu