Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

Dakarun Kamaru sun kashe ‘yan Boko Haram takwas

A kasar Cameroon Rahotanni na nuna cewar jami’an tsaro sun yi arangama da wasu da ake zaton ‘ya’yan kungiyar Boko Haram ne inda har suka kashe takwas daga cikinsu.

Dakarun kasar Kamaru
Dakarun kasar Kamaru Reuters
Talla

Arewacin kasar Kamaru ya kasance yana fama da matsalolin tsaro na hare hare da ‘yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa, lamarin da ke bayar da damar yin garkuwa da mutane.

Wata majiya kwakwara ta bayyana cewa a lokacin da dakarun Kamaru ke sintiri a kusa da garin Mora ne suka yi kicibis da ‘yan kungiyar, lamarin da ya haifar da arangama tsakanin bangarorin biyu.

 

Majiyar ta kara da cewa amma dakarun su ne suka samu galaba a fadan.
Yanzu haka bayanai na nuna cewa an kama wasu da dama daga cikin ‘yan kungiyar wadanda yawansu ya kai 48.

Kamaru ta hada iayaka da Najeriya mai tsawon kilomita 2,000.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.