Isa ga babban shafi
Mali

‘Yan tawayen Abzinawa sun fatattaki Sojin Mali a kidal

Mayakan Abzinawa a Mali sun fatattaki Sojin Mali tare da karbe ikon birnin Kidal bayan wani kazamin artabu da bangarorin biyu suka yi a tsawon yinin Laraba. Sojojin kasar da dama ne aka kashe a musayar wuta da aka yi tsakanin bangarorin biyu.

Dan tawayen Abizinawa na kungiyar MNLA a Mali
Dan tawayen Abizinawa na kungiyar MNLA a Mali REUTERS/Cheick Diouara
Talla

Shugaban kasar Mali ya yi kiran a tsagaita wuta a yankin arewacin kasar tare da ware kwanaki uku na zaman makoki daga ranar Juma’a bayan ‘Yan tawaye sun kashe tarin Sojoji.

Kakakin ‘Yan tawayen yace sun karbe ikon birane da dama da suka hada da Anderamboukane da Menaka da Aguelhoc da Tessalit.

Mohamed Ag Rhissa, daya daga cikin shugabannin MNLA ya shaidawa Kamfanin dillacin labaran Faransa cewa suna rike da ikon Kidal da fursunoni.

An dai share tsawon yinin Laraba ana gwabza fada a tsakanin ‘yan tawayen da kuma dakarun gwamnati a birnin na Kidal, a daidai lokacin da dakarun na gwamnatin suka sanar da kaddamar da farmaki da nufin kwace birnin daga hannun magoya bayan kungiyar MNLA.

Shaidun ganin da ido sun ce kafin marecen Laraba, mafi yawa daga cikin unguwannin Kidal sun fada hannun ‘yan tawaye, bayan da suka fatattaki sojan na gwamnati daga barikoki biyu da ke birnin.

Sai dai kuma Mayakan na MNLA ba su tunkari barikin Sojan Faransa ba da na Majalisar Dinkin Duniya ba da ke cikin birnin ba, yayin da wata majiyar ke cewa wasu sojojin a cikin manyan motocin yaki 27 masu sulke sun arce tare da neman mafaka a cikin rundunar Majalisar Dinkin Duniya.

A ranar Assabar da ta gabata ne dai gwamnatin Bamako ta tura dimbin sojoji zuwa wannan gari da ake kallo a matsayin babbar cibiyar Azbinawan da ke neman kafa ‘yantacciyar kasar Azawad, bayan da suka yi yunkurin hana wa Firaministan kasar Moussa Mara kai ziyara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.