Isa ga babban shafi
Nigeria

Shehun Borno ya bukaci a gudanar da azumin kwana uku

A Tarrayar Nigeria sakamakon tashe tashen hankulan da ke ci gaba da lakume rayukan mutane musamman ma a yankin arewacin kasar, yanzu haka babban malami kuma Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garba El-Kanemi, ya bukaci alummar yankin da su gudanar da azumi har na tsawon kwanaki uku daga wannan talata.

Kofar shiga Maiduguri
Kofar shiga Maiduguri REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Babbar manufar kiran ga jama’a domin su gudanar da wannan azumi ita ce, isar da kukansu ga Ubangiji Allah Madaukakin Sarki domin kawo karshen wannan matsala.

Jama’a da dama da Rediyo Faransa RFI, ya tuntuba, sun bayyana cewa sun karbi wannan kira na Shehun Borno, ta la’akari da cewa duk da cewa akwai dubban jami’an tsaro da suka hada da sojoji da kuma ‘yan sanda a yankin, to amma kusa kowace rana ana samun asarar rayukan jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.