Isa ga babban shafi
Algeria

Algeria: 'Yan takara 10 zasu fafata da Bouteflika

Akalla mutane 100 ne aka ruwaito sun janye daga shiga takarar zaben shugabancin kasar Algeria yayin da ake ci gaba da sukar takarar Abdel’aziz Bouteflika wanda ya kwashe shekaru 15 yana shugabanci a kasar.

Shugaban kasar Algeria, Abdelaziz Bouteflika
Shugaban kasar Algeria, Abdelaziz Bouteflika REUTERS/Louafi Larbi
Talla

Masana sun bayyana cewar muddin shugaba Bouteflika ya ci gaba da samun wannan gagarumar goyon bayan to akwai alamun zai lashe zaben na ranar 17 ga watan gobe.

Wata kafar yada labarai a kasar Algeria ta ruwaito cewa akwai ‘Yan takara guda 10 da suka yanki rijistar tsayawa takarar zaben shugaban kasa.

Akwai kwanaki 10 da Majalisar tsarin mulkin kasar Algeria zata kwashe domin tantance ‘Yan takara da zasu fara yakin neman zaben a ranar 23 ga watan Maris.

Bouteflika, ya bayyana kudirin tsayawa takara a kafar Telebijin wanda shi ne karon farko da shugaban ya fito a bainar Jama’a tun lokacin da ya dawo daga jinya a asibitin kasar Faransa.

Ali Benflis, tsohon Firaminista yana cikin wadanda suka yanki rijistar tsayawa takara wanda ya yi gargadi akan yiyuwar yin magudi a zaben.

Akwai sauran ‘Yan takara da suka hada da Mohamed Benhamou, da Moussa Touati da Abdelaziz Belaid da Ali Zaghdoud da kuma
Louisa Hanoune.

Kasar Algeria dai ta yi kokarin kaucewa juyin juya halin da ya rutsa da sauran kasashen larabawa irinsu Libya da Tunisia da Masar wanda ya ke daya daga cikin nasarorin da ake dangatawa da shugaba Bouteflika da ke fama da rashin lafiya yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.