Isa ga babban shafi
Najeriya

Karancin Fetir ya sa Najeriya ta fitar da ajiyarta

Gwamnatin Najeriya tace ta bude rumbun ajiyayyen Mai domin magance matsalar karancin fetir da ake ciki a cikin kasar. Kakakin Kamfanin NNPC ya shaidawa sashen Hausa na Rediyo Faransa cewa sun fitar da litar mai Miliyan 33 na Fetir a yau Talata.

Tankar Mai a harabar ginin Kamfanin NNPC
Tankar Mai a harabar ginin Kamfanin NNPC Getty Images/Suzanne Plunkett
Talla

“Mai zai wadatu a Lagos” a cewar Umar Faruk saboda sun fitar da mai a sassan yankunan Jahar.

Tun a makon jiya ne aka shiga matsalar Mai a Jahar Lagos cibiyar kasuwancin kasar bayan an shafe mako ana fama da matsalar a yankin arewaci inda farashin ya haura da kusan kashi 50.

"Ba rashin Fetir ba ne ya sa aka shiga matsalar illa wasu sun yi tunanin gwamnati zata yi karin farashin kudin Mai" a cewar Kakakin Kamfanin NNPC.

Tun da farko dai ‘Yan kasuwa da masu dakon mai a Najeriya sun daura laifin matsalar karancin fetir din ga kamfanin NNPC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.