Isa ga babban shafi
Tunisia

An ceto 'yan gudun hijira da dama a bakin ruwan kasar Tunisia

Sojin Ruwan kasar Tunisia sun yi nasarar ceto ‘yan gudun Hijira 98 na yankin Sahara da suka hada da wani Yaro dan Shekara 9 daga kasar Congo wanda ke cikin mawuyacin hali.An dai hango wadannan ‘yan gudun Hijirar ne jim kadan da Jirginsu ya shiga gabar ruwan kasar kuma ‘yan gudun hijira ne da suka hada da mutane daga kassahe daban daban, da suka tashi daga kasar Libya a cikin wani budadden Jirgin Ruwa.Mai yuwuwa ne ‘yan gudun hijirar sun nufi tsibirin Lampedusan kasar Italiya, da ake yawan samun ‘yan gudun hijira daga Africa na zuwa.Mai Magana da yawun Sojin Ruwan kasar ta Tunisia Taoufik Rahmouni ya ce an ankarar da Dakarun Sojin Ruwan kasar ne suka nufi wurin, amma suka tarar da Jirgin ba kowa a ciki, ‘yan gudun hijirar kuwa sun labe a karkashin wata ‘yar Rumfa da ke kusa da tsibirin Djerba na yankin Kudancin kasar.Daga cikin mutanen akwai Mata da wani dan karamin Yaro da ke cikin mawucin hali da aka kwasa zuwa Assibiti cikin hanzari, sauran kuwa aka dauke su zuwa birnin Sfax da ke kusa da wurin.A cikin Watan Okotoba ma an samu akalla mutane 600 a jiragen Ruwa 2, da suka nutse a ruwa, kuma mafi yawancinsu daga Eritria da Syria. 

Wasu 'yan gudun hijira suna tafiya a tsakiyar teku
Wasu 'yan gudun hijira suna tafiya a tsakiyar teku REUTERS/Marina Militare/Handout via Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.