Myanmar
Kwale kwale ya kife da Musulmi 'yan gudun hijira a Burma
Rahotanni daga kasar Myanmar sun ce, wani kwale kwale mai dauke da Musulmi, ‘Yan kabilar Rohingya, dake tserewa hare haren da mabiya addinin Budha ke kai musu, mai dauke da mutane kusan 200 ya kife.Kungiyoyin agaji sun ce, mutanen na kokarin barin garin Pauktaw ne, dake Jihar Rakhine, lokacin da aka samu hadarin.Rahotanni sun ce, dubun dubatan Musulmi na zaune a sansanin wucin gadi bayan tserewa daga gidajen su, sakamakon rikicin addinin kasar ta Myanmar, da a baya ake kira Burma.A ‘yan kwanakin nan, an kashe daruruwan Musulmi a kasar da ke yankin Asiya.
Wallafawa ranar: