Isa ga babban shafi
Najeriya

Za’a gudanar da binciken kashe kashe a Najeriya

Hukumar kare haƙƙin bil’adama ta gwamnatin Najeriya tace zata gudanar da bincike a game da kisan da ake zargin cewa gwamnatocin kasar sun aikata akan abokan hamayya tun a zamanin mulkin Soja a shekaru 20 da suka gabata.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Reuters/Tiksa Negeri/Files
Talla

Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama ta kasar tace binciken zai shafi kisan da aka yi wa jama’a ne tun daga lokacin mulkin Marigayi Janar Sani Abacha har zuwa Mulkin Cif Olusegun Obasanjo da kuma gwamnatin da ke kan karagar mulki a yanzu, kuma hukumar za ta shirya zama na musamman a bainar jama’a domin sauraren ƙorafe-ƙorafe dangane da zarge-zargen da zasu biyo baya.

Wannan mataki dai na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo ya zargi gwamnatin Jonathan da shirya kashe abokan hamayya na siyasa a wasiƙar da ya rubuta wa shugaban a kwanakin da suka gabata.

Tuni dai Gwamnatin Jonathan ta ƙaryata zargin a cikin wasikar martani da aka aikawa Obasanjo.

Sai dai Kungiyar Kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International da takwararta ta Human Rights Watch, sun buƙaci hukumar da zata gudanar da binciken ta kaucewa siyasa.

Kodayake, Shugaban hukumar Chidi Odinkalu, yace binciken ba ya da nasaba da siyasa, yana mai cewa zasu gudanar da bincike ne domin yin adalci ga waɗanda aka zalunta.

Akwai Manyan mutane da aka kashe a Najeriya da suka haɗa da Tsohon Ministan Shari’a Bola Ige da Harry Marshall da aka kashe a cikin gidansa da ke Abuja a zamanin Mulkin Obasanjo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.