Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Shugaban kasar Jamhuriyar Afruka ta tsakiya yace bai yarda kasar na shirin lalacewa ba

Shugaban Kasar Janhuriyar Afrika ta Tsakiya, Michel Djotodia, yayi watsi da ikrarin kasashen Turai cewar kasar ta kama hanyar samun fadar addinin da kuma kisan kare dangi

Shugaban kasar Jamhuriyar Africa ta tsakiya Mikael Djotodia
Shugaban kasar Jamhuriyar Africa ta tsakiya Mikael Djotodia rfi.fr
Talla

Shugaban kasar Jamhuriyar Afruka ta tsakiyar Michel Djotodia, ya ki amincewa da zargin samun fadan Addini a cikin kasar, inda yake cewa abinda ke faruwa yanzu haka, fada ne tsakanin magoya bayan tsohuwar gwamnati da ‘Yan tawayen Seleka.

Djotodia ya ce shi a ganin shi, babu abinda za’a kira kisan kare-dangi a kasar, sai dai ramuwar gayace kawai daga bangarorin guda Biyu, wanda ya zargi kasahsen duniya da neman haifar da matsala a cikin kasar.

Kwamishiniyar kula da jinkai ta kungiyar kasashen Turai, Kristalina Georgieva ta bayyana damuwar yankin kan halin da ake ciki a kasar, ganin yadda ake cigaba da samun tashin hankali da kuma rasa Rayuka daga bangaren tsohon shugaban kasa Francois Bozize da kuma bangaren Yan Tawayen Seleka masu gwamnati.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.