Isa ga babban shafi
Mali

Alkalin kotu ya bayar da umurnin tsare Janar Sanogo

To rahotanni daga kasar Mali na cewa alkalin kotu a birnin Bamako, ya bayar da umurnin tsare tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Janar Amadou Haya Sanogo, bayan da aka gabatar da shi a gabansa a yau laraba.

Tsohon shugaban gwamnatin sojan Mali, Janar Amadou Sanogo
Tsohon shugaban gwamnatin sojan Mali, Janar Amadou Sanogo Reuters/Luc Gnago
Talla

Alkalin kotun mai suna Yaya Karembe, ya bayar da umurnin tsare tsohon shugaban ne wanda jami’an tsaro suka kama da karfi bayan da ya ki karba umurnin Kotun na ya bayyana a gabansa makwanni biyu da suka wuce.

Har ila yau jami’an tsaro sun gudanar da bincike a gidan janar Sanogo wanda ake zargi da hannu wajen kashe wasu sojoji 6 a lokacin wani bore da aka yi cikin barikin sojan Kati da yake jagoranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.