Isa ga babban shafi
Masar

Hadaddiyar Daular Larabawa ta baiwa Masar tallafin kudi

Kasar Hadaddiyar daular larabawa ta bai wa gwamnatin mulkin sojan kasar Masar karin gudunmuwar dalar Amurka milyan dubu uku da milyan dari tara, domin ci gaba da tsayuwa a kan duga duganta. Ita dai kasar ta daular larabawa, ita ce ta farko a cikin kasashen yankin Gulf da ta fito fili ta fara bayyana goyon bayanta ga juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin dimokuradiyya ta Mohammad Morsi a ranar 3 ga watan julin da ya gabata.Tun bayan wancan juyin mulkin, kasar ta Masar ke ci gaba da fuskantar zanga zanga, da kashe kashe a yankunan ta da dama.‘Yan kungiyar ‘yan uwa musulmi ta hambararren shugaba Mohamed morsi ne, ke ke ci gaba da nuna kin amincewar su da gwamnatin mulkin sojan da aka kafa tun bayan juyin mulki, inda suke kallon gwamnatin a matsyin haramtacciya. 

Shugaban rikon kasar Masar, Adly Mansour
Shugaban rikon kasar Masar, Adly Mansour Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.