Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji sun ce sun kashe ‘Yan Boko Haram 37 a Najeriya

Dakarun Najeriya sun tabbatar da kashe wasu da suka ce ‘yan kungiyar Boko Haram ne akalla 37 a wani ruwan wuta da suka yi wa sansanin ‘Yan kungiyar ta kasa da kuma jiragen sama a Jahar Borno. Kakakin rundunar Sojin, Aliyu Danja yace sun kwace makamai da bindigogi tare da tarwatse motoci da babur na ‘Yan Kungiyar.

Sojin Najeriya a garin Maiduguri.
Sojin Najeriya a garin Maiduguri. AFP
Talla

Samamen da Sojojin suka kai yazo ne bayan wani hari da wasu ‘Yan bindiga da ake zaton ‘Yan Boko Haram ne suka kai akan iyaka da Kamaru inda suka bindige mutane 19 sanye da kayan Sojoji.

Jahar Borno dai ta kasance sansanin kungiyar Boko Haram a shekaru hudu da suka gabata.

Akalla mutane sama da 3000 cikin su har da yara ‘yan makaranta ne aka ce sun rasa rayukansu a hare haren da kungiyar ke ci gaba da kai wa tare da salwantar da dukiyar jama’a da dama a Tarrayar Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.