Isa ga babban shafi
Sierra Leon

An tabbatar da hukumcin daurin shekaru 50 ga tsohon shugaban kasar Laberiya Chals Taylor

Wata kotun kasar Saliyo, karkashin Majalisar dinkin Duniya, ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 50, da aka yanke wa tsohon shugaban kasar Liberia Chales Taylor. Kungiyar kare hakkin dan adam ta Duniya Amnesty International, tace hukuncin ya nuna wa shugabani a kasashen duniya cewa, ba wanda ya fi karfin doka.  

Talla

Wannan hukuncin mai cike da tarihi, ya kawo karshen shekaru 7 da aka shafe kan sharia’ar tsohon dan kama karyan, na kasar Liberia.
 

Da alama kuma zai karashe rayuwar shi a wani gidan yarin wata kasar waje, watakila Britaniya.
 

A shekarar 2012, aka kama Taylor mai shekaru a duniya, 65, da laifin mara wa ‘yan tawayen kasar Saliyo baya, a yakin da aka gwabza a kasar, tskanin shakarun 1991 zuwav 2002, da ya lakume rayukan mutane dubu 120.

Sai dai Chales taylor ya yi ta musanta zargin da aka mishi na aikata laifukan yaki a kasar, da ke makwabta da Liberia, tare da hadin bakin kungiyar ‘yan tawayen Revolutionary United Front.
 

A tsakiyar shekarar 2006, aka kama Chales Taylor, aka kuma mika shi zuwa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague, ko La Hegue, kuma a watan mayun shekarar bara, aka yanke mishi hukunci, kan daya daga cikin mugan laifukan da aka yi kan bil adama a tarihi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.