Mali
An yi zanga-zanga a garin Kidal dake Mali
Ministan sasanta 'Yan kasar Mali, Sheikh Oumar Diarra, ya ce shirin su na hada kan al’ummar kasar na nan kan hanya, duk da hargitsin da aka samu a karshen mako, lokacin da masu zanga zanga suka tarbe su da ruwan duwatsu a Kidal.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Masu zanga zangar na adawa da ziyarar jami’an gwamnatin kafin fara tattaunawar da aka shirya, a yarjejeniyar da suka sanya hannu kafin zaben kasar.
Rahotanni sun ce, an farfasa jerin motocin ministocin da suka ziyarci garin Kidal.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu