Isa ga babban shafi
Nijar

Sabon rikicin siyasa a Nijar bayan ficewar jam'iyyar Lumana daga gwamnati

A Jamhuriyar Nijar, jam’iyyar Lumana, wadda ita ce babbar abokiyar kawance ga jam’iyyar PNDS Tarayya ta shugaba Issifu Mahamadou, ta bayyana dalilanta na janyewa daga gwamnatin kawance da aka kafa a kasar.

Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Nijar
Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Nijar France 24
Talla

A wata sanarwa da ta fitar dangane a karshen mako, jami’iyyar ta Lumana, ta ce kfa sabuwar gwamnatin hadin kan kasar da shugaban Issifou ya yi, na a matsayin cin mutunci ga jam’iyyarsu da kuma shugabanta Hama Amadou.

Har ila yau jam’iyyar ta Lumana wadda ta marawa PNDS Tarayyar bayan domin samun nasarar Issifou Mahamadou a zaben da aka gudanar a kasar a shekara ta 2011, ta yi zargin cewa an kwace muhimman mukamai daga hannun magoya bayanta domin danka su a hannu magoya bayan wata jam’iyyar da ba ta taka rawa wajen zaben Issifou Mahamadou ba.

Tuni dai PNDS Tarayya ta shugaban kasar ta mayar da martani dangane da wannan mataki na Lumana, inda ta bukaci jam’iyyar da ta dawo a cikin gwamnati domin ci gaba da aikin gina kasar, sannan kuma ta bukaci ‘yan kasar da su kwantar da hankulansu domin kuwa lamari ne da za a warware a cikin gajeran lokaci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.