Isa ga babban shafi
Libya

Shugaban Majalisar Dokokin Libya ya sauka daga mukaminsa

A kasar Libya sakamakon dokar haramta wa duk wadanda suka yi aiki tare da marigayi Mo’ammar Gaddafi, ala tilas su sauka daga kan mukamansu, a yau Shugaban Majalisar Dokokin kasar Mohammed al-Megaryef ya ajiye aikinsa.

Masu zanga-zangar neman tube tsoffin jami'an Kaddafi daga mukaman gwamnati.
Masu zanga-zangar neman tube tsoffin jami'an Kaddafi daga mukaman gwamnati. Reuters/Ismail Zitouny
Talla

Jim kadan kafin saukarsa, Almegryef ya fadawa zaman majalisar cewa kowa ya dace ya mutunta doka saboda haka ya ajiye aikin nasa kasancewar ya yi aiki da marigayi Moammar Gaddafi, a matsayin jakada.

Batun tilasta wa wadanda suka yi aiki da marigayi Kaddafi sauka daga kan mukamansu, na daga cikin abubuwan da matasan kasar ke bukata, inda ko a cikin kwanakin da suka gabata, wasu daruruwa dauke da makamai suka mamaye ginin ma’aikatar harkokin wajen kasar da kuma wasu muhimman cibiyoyin gwamnati dauke da makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.