Isa ga babban shafi
Libya

Matasa dauke da makamai sun mamaye ma'aikatar harkokin wajen Libya

Wasu mutane dauke da makamai sun yi wa ginin ma’aikatar harkokinn wajen kasar Libya da ke birnin Tripoli kawanya, inda suka bukaci a tube dukkanin jami’an gwamnatin tsohon shugaban kasar Kanar Mu’ammar Kaddafi daga manyan mukamai a kasar.

Masu zanga-zanga a birnin Tripoli
Masu zanga-zanga a birnin Tripoli REUTERS/Omar Ibrahim
Talla

Rahotanni sun ce mutane akalla 200 a cikin motocin Pick-Up guda 20 ne, dauke da bindigogi da kuma rokoki suka yi wa ginin kawanya, yayin da wasu da dama daga cikinsu suka ja daga a kan hanyoyin da ke isa zuwa ga ginin.
Tun dai bayan kifar da gwamnatin shugaba Kaddafi ne, kasar ta Libya ta kara fadawa wani hali na rashin tabbas, sakamakon yadda mayakan sa-kai ke ci gaba da iko da yankuna daban daban na kasar ba tare da kin yi wa gwamnatin Tripoli biyayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.