Isa ga babban shafi
Chadi

An yi yunkurin juyin mulki a Chadi

HUKUMOMIN Kasar Chadi sun sanar da bankado wani yunkurin juyin mulki a kasar.Jami’an tsaron kasar sunm ce lamarin ya kai ga kama wasu jami’an soji.Rahotanni sun ce, an yi yunkurin ne jiya Larba, kuma an kama mutane da dama cikin su harda wani Dan Majalisa daga bangaren 'Yan adawa, mai suna Saleh Makki.Ministan sadarwan kasar, Hassan Sylla Bakary ya ce mutanen sun shafe watanni suna kitsa yunkurin kifar da gwamnatin Idriss Deby.Kasar Chadi, mai fama da talauci, da ke yankin yammacin Africa, ta yi ta fama da juye-juyen mulki, da ‘yan tawaye a baya.Shi kanshi shugaba Idriss Deby ‘yan tawaye ya jagoranta zuwa birnin N'Djamena, ya karbe mulki da tsini bindiga a shekarar 1990.Ko a makon da ya gabata sai da shugaba Deby ya zargi makwabciyar kasar shi Libya, da barin ‘yan tawayen kasar su kafa sansanin horaswan su a kasar, inda yace suna shirin kifar da gwamnatin shi, sai dai hukumomin Libya sun musanta zargin. 

Shugaban kasar Chadi Idriss Déby Itno.
Shugaban kasar Chadi Idriss Déby Itno. Photo AFP / Martin Bureau
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.