Isa ga babban shafi
Chadi

‘Yan tawayen Chadi za su sake rungumar makamai domin yaki da Deby

‘Yan tawayen Chadi sun ce za su sake rungumar makamai domin yaki da shugaba Idriss Deby saboda ya kasa sasantawa da su tun lokacin da suka amince su ajiye makamai shekaru biyu da suka gabata.

Shugaban 'Yan tawayen Chadi Timane Erdimi tare da dakarun shi da ke yaki da gwamnatin Idriss Déby.
Shugaban 'Yan tawayen Chadi Timane Erdimi tare da dakarun shi da ke yaki da gwamnatin Idriss Déby. (Photo : Laurent Correau/ RFI)
Talla

‘Yan tawayen sun ajiye makamai ne tun lokacin da gwamnatocin Chadi da Sudan suka kawo karshen yaki tsakaninsu a shekarar 2010.

Kasashen biyu kuma sun amince da yarjejeniyar tsaro a kan iyakokinsu.

Amma Shugaban ‘Yan tawayen Chadi Timane Erdimi ya shedawa kamfanin Dillacin labaran Reuters cewa bayan kwashe shekaru biyu sun gaji da jira.

Kasar Chadi dai na daya daga cikin kasashen da ke fama da talauci a Nahiyar Afrika saboda rikici a yankunan gabaci da kudancin kasar.

A shekarar 1990 ne Idriss Deby ya karbi ragamar shugabancin kasar Chadi bayan ya jagoranci juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.