Bozize ya zargi kasar Chadi da taimakawa ‘Yan tawayen da suka hambarar da gwamnatin shi
Hambararren shugaban kasar Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiyar, Francois Bozize ya yi zargin cewa kasar Chad ice ta taimakwa ‘Yan tawayen Seleka suka hambarar da gwamnatin shi kamar yadda A cewar rahotanni suka nuna.
Wallafawa ranar:
A cewar shi, kamin hambarar da gwamnatin ta shi, dakarun kasar sun samu nasara akan ‘Yan kungiyar ta Seleka.
‘‘Mun samu galaba akan dakarun Seleka a ranar Assabar amma kuma daga baya mun san akwai taimako da suka samu daga wata kasar Afrika kuma na yi imanin kasar Chadi ce.’’ Inji Bozize
Wannan dai shine karo na farko da Bozize ya fito ya yi magana a kafar yada labarai tun bayan hambarar da gwamnatin shi.
Gwamnatin Chadi dai ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakwa Bozize a shekarun day a kwashe yana shugabanci a kasar tare da taimaka masa hambarar da gwamnatin kasar a shekarar 2003.
Izuwa hada wannan rahoto gwamnatin ta Chadi ba ta mayar da martani akan wannan zargi na Bozize ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu