Ntaganda ya gurfana a gaban kotun manyan laifuka ta duniya
Madugun ‘Yan-tawayen kasar Jamhuriyar Demokardiyar Congo, Bosco Ntanganda, da ake zargi da hannu wajen laifukan yaki, yanzu haka na gaban Kotun kasa-da-kasa da ke Hague domin sauraron irin hukuncin da za a yi masa.Ntanganda wanda a tarihin kotun shine na farko da ya mika kansa gaban kotun da ta dade tana cigiyarsa, ya kwana tsare hannun kotun ne, bayan ya mika kansa.
Wallafawa ranar:
Ntanganda wanda akewa lakabi da “Terminator” tun ranar Litini wancan makon ya kai kansa ofishin jakadancin Amurka dake Rwanda, inda ya nemi su kaishi Kotun kasa-da-kasa dake Hague.
Yanzu haka dai yana tsare a hannun kotun dake Hague.
Ana zarginsa ne da yin sanadin kisan mutane akalla 800 mazauna kauyuka a kasar ta Congo, sannan kuma ya rika diban ‘yan kana nan yara aikin soja, da gallazawa mata , duk a tsakanin 2002-2003.
Ya kasance na biyar dan Afrika dake gaban wannan kotun, da za ta fara sauraron laifinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu