Isa ga babban shafi
Janhuriyar Afrika ta Tsakiya

'Yan tawaye sun kwace fadar shugaban Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

Mayakan kawancen ‘yan tawayen Saleka a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar sun sanar da kwace fadar shugaban kasar da ke birnin Bangui a sanyin safiyar yau.

François Bozizé, à birnin Bangui
François Bozizé, à birnin Bangui REUTERS/Luc Gnago
Talla

Daya daga cikin manyan kwamandojin ‘yan tawayen kamar Djouma Narkoyo, ya tababatar wa kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa AFP cewa, kwace fadar ya biyo bayan wani mummunan artabun da aka yi ne tsakanin dakarun da ke biyayya ga shugaban kasar da kuma dakarunsu.

Kwamandan ‘yan tawayen ya ce a lokacin da suka shiga fada, tuni shugaban kasar Francois Buzize ya riga ya fice daga ciki, yayin da wasu rahotanni ke cewa tuni shugaban ya isa a kasar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.