Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Bozize ya rusa majalisar ministocinsa

Bayan cimma yarjejeniya da aka yi a Janhuriyar Afrika ta Tsakiya, Shugaban kasar, Francois Bozize ,ya rusa majalisar ministocin sa dan kafa gwamnatin rikon kwarya. A yarjejeniyar, sabuwar gwamnatin da aka kafa zata sami jagorancin daya daga cikin ‘yan adawa ne ,sannan kuma zai kai kasar ga zaben majalisa a cikin makwanin goma sha biyu.  

Shugaban kasar Janhuriyar Afrika ta Tsakiya, Francois Bozize
Shugaban kasar Janhuriyar Afrika ta Tsakiya, Francois Bozize REUTERS/Luc Gnago
Talla

Hakan zai sa a maye gurbin majalisar dattawa da sakamakon hakan ‘yan tawayen suka yi alkawarin tsagaita buda wuta, wanda shine babban kalubale da shugaba Bozize ke fuskanta.

Hakan zai bashi daman cika wa’adin shi da zai zo karshe a shekara ta 2016

Sai dai kuma,’yan tawayen sun yi gargadi cewar zasu kara daukan makamai muddin gwamnatin ta sabawa yarjejeniyoyin tattaunawar da suka shafi janye dakarun kasashen waje da suke karfafa sojojin kasar, da kuma sakin wasu ‘yan gidan kaso da aka tsare bisa laifukan dake da alaka da siyasa.

Kungiyar ‘yan tawayen, wacce ake wa lakabi da Seleka ta kunshi kungiyoyi biyar ‘yan tawaye sun buda wuta a kasar ne bisa zargin Bozize da watsi da yayi a tattaunawar su ta zaman lafiya a shekara ta 2007.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.