Isa ga babban shafi
Najeriya-Faransa-Kamaru

An tsallaka da Faransawan da aka yi garkuwa da su zuwa Najeriya daga Kamaru

Gwamnatin Kasar Kamaru tace ‘Yan Bindigar da suka yi garkuwa da ‘Yan kasar Faransa bakwai, sun tsallaka da su zuwa Najeriya. Ma’aikatar harkokin wajen Kamaru tace an yi garkuwa da mutanen ne a Sabon Gari da ke kusa da kauyen Dabanga, a kan iyakar kasashen biyu.

Gidan ajiye Dabbobi da ake kira Waza Park, a kasar Kamaru
Gidan ajiye Dabbobi da ake kira Waza Park, a kasar Kamaru Amcaja/CC
Talla

"Wannan aiki ne na wata kungiyar ‘Yan ta’adda da muka san da zamanta a tarayyar Najeriya" inji shugaba Francois Hollande wanda ke zantawa da manema a birnin Athens na kasar Girka

A lokacin da aka tambaye Shugaba Hollande, ko akwai wata alaka tsakanin sace mutanen da kuma yakin da Faransa ke jagoranta a Mali ?, Sai Shugban ya fito fili ya ambaci sunan Boko Haram a matsayin Kungiyar da ya ke zargi da aikata hakan, yayin da majiyoyin tsaro a kasar ta Kamaru ke cewa akwai yiyuwar wannan kungiyar ce ta sace Fansawan.

Mahukuntan Kasar Kamaru sun yi zargin ‘Yan Fashin jiragen ruwa ne ke kai hare hare da Garkuwa da mutane a yankin Bakassi da ke kan iyakokin kasashen biyu.

A watan Disemba an taba yin garkuwa da wani Bafaranshe Francis Collomp wanda kungiyar Ansaru a Najeriya ta dauki alhaki.

A ranar Litinin Kungiyar Ansaru ta dauki alhakin yin garkuwa da wasu Turawa guda Bakwai Ma’aikatan Kamfanin Setraco a garin Jama’are da ke jahar Bauchi a Arewacin Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.