An wawushe dukiyar Larabawa da Abzinawa a Gao bayan ficewar ‘Yan tawayen Mali
Babu abinda ya rage a shagunan Tsirarun Larabawa da ke kasuwanci a birnin Gao bayan wasu mazauna garin sun wawushe dukiyarsu saboda zargin suna taimakawa Mayakan Ansar Dine da suka karbe ikon Yankin Arewacin Mali tsawon watanni Tara.
Wallafawa ranar:
Tun bayan da Dakarun Faransa da Mali suka karbe ikon Gao daga Mayakan Mali, Larabawa da Abzinawa ke fuskantar fashi daga matasan garin.
Tuni Larabwa suka fice daga Gao domin tsira da rayuwarsu.
Nisan Kilomita 1,200 ne tsakanin Gao zuwa Bamako babban birnin kasar Mali. Kuma Rahotanni sun ce kimanin mutane 350,000 suka fice bayan ‘Yan tawaye sun karbe ikon garin.
Tun a farko Faransa da Amurka da Tarayyar Turai suka yi gargadin za'a iya kai hare haren ramuwar gayya ga tsirarun Larabwa da abzinawa idan aka karbe ikon biranen Gao da Timbuktu da Kidal.
Majalisar Dinkin Duniya ta fara shirye shiryen aikawa da Dakaru domin karbe ragamar tafiyar da tsaro daga hannun dakarun Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu