Isa ga babban shafi
Burundi-Tanzania-RFI

Kotun Burundi ta yankewa Ruvakuki hukuncin shekaru uku a gidan yari

Wata Kotun daukaka kara a kasar Burundi ta yankewa wani Dan jarida mai aiki tare da Gidan Radiyo Faransa (RFI) a sashin Swahili, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru uku. Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta sassauta tuhumar da ake wa Hassan Ruvakuki, daga yunkurin aikata ayyukan ta’addanci zuwa yin mu’amulla da haramtacciyar kungiyar 'Yan tawaye.  

Wakilin RFI a Sashen Swahili  Hassan Ruvakuki, Dan jaridar kasar Burundi
Wakilin RFI a Sashen Swahili Hassan Ruvakuki, Dan jaridar kasar Burundi AFP PHOTO/Esdras Ndikumana
Talla

A watan Yunin da bara ne, wata kotu a kasar ta Burundi ta yanke mai hukunci daurin rai da rai, hukunci da kafofin yada labarai suka yi Allah wadai da shi.

Da farko ana zargin Ruvakuki ne da yunkurin aikata ayyukan kai hare-hare tare da kungiyar dake dauke da makamai a Gabashin Cankuzo dake kusa da kasar Tanzania inda mutane da dama suka rasa rayukansu a rikice - rikice.

Ruvakuki wanda baya cikin kotun a lokacin da aka yanke mai wannan hukunci, ya dade yana bayyana gaskiyarsa akan wannan lamari.

Har ila yau, kungiyoyin 'Yan jarida dama a duk fadin duniya sun nuna rashin jin dadinsu da wannan hukunci na baya bayannan inda suke nuna cewa, Ruvakuki na gudanar da aikinsa ne kawai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.