Isa ga babban shafi
Burundi-Tanzania

Kotun Burundi ta yanke wa Dan Jaridar RFI hukuncin dauri rai da rai

Hassan Ruvakuki, ma’aikacin Radiyo Faransa RFI a Sashen Swahili yana cikin Mutane  13 da kotun Burundi ta yanke wa hukuncin daurin Rai da Rai a gidan Yari bayan samun shi da laifin zantawa da ‘Yan Tawaye. Ruvakuki yace zai daukaka kara domin kalubalantar hukuncin kotun

Hassan Ruvakuki Wakilin Rediyo Faransa a sashen Swahili da aka kama a Burundi
Hassan Ruvakuki Wakilin Rediyo Faransa a sashen Swahili da aka kama a Burundi RFI
Talla

Dan Jaridan yana aiki ne a matsayin wakilin Sashen Swahili na Radio Faransa, da tashar Bonesha FM a Bujumbura.

Gidan Radio Faransa da Kungiyar Reporters Without Borders, sun bayyana kaduwarsu da hukuncin.

Ruvakuki wanda dan asalin kasar Burundi ne, Kotun ta kama shi da laifin taimakawa ‘Yan Tawayen Burundi a Tanzania bayan Cafke shi aBujumbura babban birnin Burundi a watan Nuwamban Bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.