Isa ga babban shafi
Tanzania-Burundi

Shekara guda ke nan da aka kama Wakilin RFI Ruvakuki

A rana irin ta yau ne 28 ga watan Nuwamba a shekarar 2011 aka kama Wakilin RFI a sashen Swahili Hassan Ruvakuki a kan zargin yana da alaka da ‘Yan tawayen Burundi a lokacin da kai ziyara Tanzania domin gudanar da aikin shi. An yanke wa Ravakuki hukuncin daurin rai da rai.

Wakilin RFI a Sashen Swahili  Hassan Ruvakuki, Dan jaridar kasar Burundi
Wakilin RFI a Sashen Swahili Hassan Ruvakuki, Dan jaridar kasar Burundi AFP PHOTO/Esdras Ndikumana
Talla

A ranar Takwas ga watan Janairu ne ake sa ran kotu za ta sake zaunawa domin diba hukuncin bayan dan Jaridar ya daukaka kara. Abokan aikin Ravakuki a gidan Rediyon FM na Bonesha sun yi Allah waddai da rashin adalcin da aka yi wa Dan jaridar.

A ranar 28 ga watan Nuwamba ne a shekarar 2011 ‘Yan sanda suka Cafke Ruvakuki kuma yanzu babu wani labari game da inda ake tsare da shi.

Hassan dai ya fuskanci barazana ne daga Mahukuntan Tanzania wadanda suka bukaci lalle sai ya bayar da bayanai game da ‘Yan tawaye bayan ya gana da shugabanninsu.

Bayan cafke shi, a ranar 20 ga watan Yunin bana ne Kotu ta yanke wa Ruvakuki hukuncin daurin rai da rai akan laifin Ta’addanci, hukuncin da kungiyar kare ‘Yan Jaridu ta duniya ke kalubalanta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.