Isa ga babban shafi
Mali

Mayakan Ansar Dine sun kori ‘Yan tawayen Abzinawa a Arewacin Mali

Rahotanni sun ce, kungiyar Ansar Dine ta yi nasara korar ‘Yan Tawayen Abzinawa daga garin Gao, da ke Arewacin Mali, a dai dai lokacin da ministocin kungiyar kasashen Turai suka amince da shirin tura jami’ai 250 da za su horar da sojojin kungiyar ECOWAS.

Mayakan kungiyar MUJAO a Mali.
Mayakan kungiyar MUJAO a Mali. AFP PHOTO / ROMARIC OLLO HIEN
Talla

Wasu Rahotannin sun ce kungiyar MUJAO ta karbe ikon garin Menaka, wanda ke hannun ‘Yan tawayen Abzinawa, kuma ana ganin hakan na iya illa ga shirin tattaunawa da kungiyoyin biyu.

Dukkanin bangarorin biyu sun tabbatar da labarin, kuma ‘Yan tawayen Abzinawa sun ce kungiyar MUJAO ta samu taimakon mayaka ne daga kungiyar Al Qaeda reshen Magrib a rikicin da ya ba su nasara.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Shugabannin kasashen Yammacin Afrika ke Shirin bin hanyoyin da za su kwace ikon yankin Arewacin da ya fada hannun Mayakan Ansar Dine da ke neman tabbatar da Shari’ar musulunci a daukacin kasar Mali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.