Isa ga babban shafi
Mali-Burkina Faso

Mai shiga tsakani a rikicin Mali zai tattauana da ‘Yan tawayen kasar.

Mai shiga tsakani a rikicin Mali, Shugaban kasar Burkino Faso, Blaise Compaore zai hadu da ‘Yan kungiyar Ansar Dine masu kishin Islama da kuma ‘Yan tawayen Taureg a karon farko domin nemo hanyar da za a magance rikicin na Mali.  

Shugaban kasar Burkino Faso, Blaise Compaore
Shugaban kasar Burkino Faso, Blaise Compaore REUTERS/Noor Khamis
Talla

Compaore dai zai gana a gobe tare da kungiyoyin biyu kamar yadda ofishinsa ya fitar a wata sanarwa.

Tattaunawar da bangarorin uku zasu yi zai zamanto wani cigaba akan kokarin da ake yi na neman bakin zaren kawo karshen rikicin na Mali, a dai dai lokacin da ake shirin aikawa da dakarun Kasa da Kasa domin su kwato yankin Arewacin kasar ta Mali dake hanun ‘Yan tawayen.

Juyin mulkin dai da sojoji suka gudanar a watan Maris na wannan shekara shi ya bawa ‘Yan tawayen tare da taimakaon Abzinawa suka mallake Arewacin na Mali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.