Isa ga babban shafi
Mali-ECOWAS

Shugabannin ECOWAS sun amince su aika da dakaru zuwa Mali domin kakkabe ‘Yan tawaye

Shugabannin Kungiyar kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS, sun amince da shirin tura dakaru 3,300 zuwa kasar Mali, don kakkabe ‘YanTawayen Ansar Dine da suka kwace ikon Yankin Arewaci bayan shugabannin sun gana a Abuja babban birnin Najeriya.

Dakarun Kungiyar ECOWAS
Dakarun Kungiyar ECOWAS dailynewsegypt.com
Talla

Shugaban kasar Cote d’Ivoire kuma Shugaban kungiyar, Alassane Ouattara ya shaida wa manema labarai cewar za su aika da Dakaru 3,300 a Mali wadanda za su kwashe shekara domin farautar ‘Yan tawaye.

A cewar Shugaba Ouattara, kasashen kungiyar ne za su hada kai domin samar da dakarun kuma suna sa ran samun karin wasu dakaru daga wasu kasashen Afrika.

Shugaban kuma yace yana fatar Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai amince da kudirin cikin gaggawa, domin dakarun su fara kaddamar da yaki.

Akwai dai kasashe da za su bayar da rundunar Soji wadanda suka hada da Najeriya da Senegal da Nijar da Burkina Faso da Ghana da Togo.

Wasu kasashen Afrika kuma da suka hada da Chad da Mauritania da Afrika ta Kudu sun ce za su bayar da nasu tallafin Soji.

Sai dai duk da amincewa da kudirin daukar matakin Soji, shugabannin kasashen sun ce tattaunawa ita ce hanya mafi kyau domin kawo karshen rikicin Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.