Isa ga babban shafi
Maroko

Mutane biyar sun bace bayan kifewar jirgin ruwa a yankin Maroko

Akalla mutane biyar ne suka bace bat bayan wani jirgin ruwa dauke da wadansu da ake kyautata zaton bakin haure ya kife a kusa da gabar Arewacin kasar Maroko, cikinsu har da mai karamin shekaru. 

Wani jirgin ruwa a yankin tekun kasar Moroko
Wani jirgin ruwa a yankin tekun kasar Moroko http://www.womenonwaves.org
Talla

Bakin haure su 17 ne suke cikin jirgin wanda aka rawaito cewa dan karami ne, a yayin da su ke kokarin shiga Melila.

Rahotanni sun nuna cewa cikin wadanda su ka bace harda manyan mata guda uku.

A lokuta da dama, bakin haure daga Nahiyar Afrika kan yi amfani da wannan yanki wajen shiga Nahiyar Turai, a dai dai lokacin da hukumomi a kasar ta Maroko ke tsaurara matakan tsaro.

A wannan shekarar kadai, daruruwan bakin haure sun bace a teku, inda dayawa har izuwa yanzu ba a ji duriyarsu ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.