Isa ga babban shafi
Libya

Gwamnatin rikon Libya zata mika mulki ga zababbiyar Majalisa

Shugabannin Gwamnatin rikon kwaryar Libya, za su mika mulki ga zababbiyar Majalisar kasa a ranar Larabam, 8 ga watan Agusta, bayan ‘Yan tawaye sun kawo karshen mulkin Kanal Gaddafi.

Wani Balaraben kasar Libya
Wani Balaraben kasar Libya REUTERS/Anis Mili
Talla

Kakakin Gwamnatin Rikon kwaryar Libya Saleh Darhoub, yace a ranar Laraba ne za su mika tafiyar da Mulki ga hannun Majalisa cikin kwanciyar hankali.

A ranar 7 ga watan Yuli ne Al’ummar kasar Libya suka kada kuri’ar zaben farko a kasar bayan kawo karshen shekaru 40 na Kanal Gaddafi.

Gwamnatin NTC za ta mika mulkin ga ‘Yan Majalisa 200 wadanda zasu jagoranci kasar har zuwa a gudanar da zabe karkashin kundin tsarin mulki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.