Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai hare haren biranen Jos da Biu a Najeriya

Kungiyar Jam’atu Ahlis Sunnah Lidda awati Wal Jihad da ake kira Boko Haram ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin kunar bakin wake da harbin bindiga a wasu Coci guda biyu a arewacin Najeriya, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane Uku. Kungiyar ta yi gargadin sake kai wasu hare haren.

Tarin mutane suna kallon motar da wani dan kunar bakin wake ya tayar da Bom a Yelwa a Najeriya
Tarin mutane suna kallon motar da wani dan kunar bakin wake ya tayar da Bom a Yelwa a Najeriya Reuters/Stringer
Talla

“Mu ne muka kai harin kunar bakin wake a Coci garin Jos da kuma wani harin a wata Coci a Biu,” inji kakakin kungiyar Abul Qaqa a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai ta wayar Salula a birnin Maiduguri.

Kungiyar tace sun kai harin ne domin kunyata Jami’an tsaro wadanda suka yi ikirarin gurgunta kungiyar.

A ranar Lahadi ne bom ya tashi da wani Dan kunar bakin wake da Motarsa a Garin Jos daga bisani ne kuma ‘Yan bindiga suka bude wuta a wata Coci a garin Biu.

Kakakin ‘Yan sandan Jahar Plateau, Abuh Emmanuel yace Bom din ya tashi ne da dan kunar bakin waken kafin ya shiga harabar Cocin evangelical a garin Jos. A cewarsa ginin Cocin baki daya ya ruguje.

Kakakin gwamnatin Jahar Plateau, Pam Ayuba yace mutane Biyu ne suka mutu a harin Jos amma mutane 41 suka samu rauni.

Shugaban kungiyar mabiya Addinin kirista a Biu, Samson Bukar yace an samu mutuwar mutum guda bayan da ‘Yan bindiga suka bude wuta a wajen ibadar Kirista.

An kwashe lokaci mai tsawo kungiyar Boko Haram tana ikirarin daukar alhakin kai hare hare a Najeriya.

A watan Janairu ne aka kai wani hari mafi muni a birnin Kano wanda ya yi sanadiyar hasarar rayuka 185.

Kuma kungiyar Boko Haram ce ta yi ikirarin kai harin ranar Kirsimeti a suleija kusa da Abuja wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 44.

03:56

Sheikh Dahuru Bauchi Malamin Addinin Islama a Najeriya

Shehu Saulawa

Yanzu haka dai babu wata alamar tattaunawa tsakanin Gwamnati da Kungiyar Boko Haram domin kawo karshen zubar da jini. Domin a makon jiya ne Kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lidda awati Wal Jihad ta musanta kalaman sheikh Dahiru Bauchi wanda ya yi ikirarin shiga tsakanin sasanta rikicin Kungiyar da Gwamnatin Tarayya.

Kungiyar Kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International tace akalla mutane 3,000 suka mutu tun fara kaddamar da hare hare a Najeriya a shekarar 2009.

Kungiyar Jam’atu Ahlis Sunnah Lidda awati Wal Jihad da aka lankaya wa sunan Boko Haram tana mayar da martani ne bisa kisan gillar da Jami’an tsaron Najeirya suka yi wa shugabansu Muhammad Yusuf a zamanin Mulkin Marigayi Ummaru Musa ‘Yar’adua.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.