Isa ga babban shafi
Najeriya

Dahiru Bauchi zai jagoranci sasanta rikicin Boko Haram a Najeriya

Gwamnatin Najeriya, tare da kungiyar Jama’atu Ahlul Sunnah Lidda’awati wal Jihad da ake kira da sunan Boko Haram, sun amince malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a matsayin mai shiga tsakanin tattaunawar da za ta haifar da sulhu a tsakanin su.

Sheikh Dahuru Bauchi Malamin Addinin Islama a Najeriya
Sheikh Dahuru Bauchi Malamin Addinin Islama a Najeriya Facebook
Talla

Sheikh Dahiru Usman Bauchi yace a matsayinsu na Malaman Addini sun dade suna neman hanyoyin da za’a yi sulhu tsakanin Boko Haram da Gwamnati saboda kawo karshen zubar da jini a Arewacin Najeriya.

Malam Dahiru Bauchi yace sun bukaci gwamnati Tarayya  rubuta wasika domin amincewar shiga tsakanin sasantawa da kungiyar Ahlul Sunnah Lidda’awati wal Jihad ta hanyar wani da ke kusa da kungiyar.

Sai dai kungiyar Ahlul Sunnah Lidda’awati wal Jihad tace akwai sharudda na sulhu da zata shata bayan sun bukaci buga wasikar Gwamnatin a Jarida domin shaida ga idon duniya.

An dade dai Gwamnatin Tarayya na yunkurin sasantawa da Kungiyar Boko Haram a Najeriya.

A wata Ziyarar da mataimakin shugaban kasa Alhaji Namadi Sambo ya kai a birnin gombe ya nemi kungiyar Boko Haram fitowa domin tattaunawa don kawo karshen jubar da jini a kasar.

Karo biyu ne Shekau ke fitowa ta kafar Bidiyo a You Tube inda ya ke ikirarin shi ne shugaban kungiyar tare da gargadin kaddamar da hare hare ga Jami’an tsaro saboda daukar fansar kisan shugaban su Muhammad Yusuf.

Bayan kai harin Kamfanin Jaridar This Day, Shekau Ya yi barazanar ci gaba da kai wasu hare hare a manyan kafafen yada labaran Najeriya da na kasashen Waje.

Sakon Bidiyo ya fara ne da Waka: “ Mu ba ‘Yan Boko Haram ba ne Sunanmu ‘Yan Najeriya, Mu musulmi ne, Ahlussunnah ku fadi gaskiya”..

A sakon Bidiyon, Imam Shekau ya yi gargadi ga Gwamnati inda yace matukar gwamnati ba ta dai na kame matansu  da yara ba, da rusa musu gidaje, to za su ci gaba da rusa gine-ginen gwamnati musamman makarantu.

An kwashe lokaci mai tsawo ana kokarin sasantawa da kungiyar Boko Haram.

A bara shekarar 2011, Hukumar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International tace sama da mutane 3,000 suka mutu tun fara kaddamar da hare haren Boko Haram a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.