Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta nisanta kanta daga kalaman Dahiru Bauchi

Kungiyar Jam’atu Ahlis Sunnah Lidda awati Wal Jihad da ake kira Boko Haram ta nisanta kanta daga kalaman Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda ya yi ikirarin kungiyar ta amince ta koma teburin tattaunawa da Gwamnatin Tarayyar Najeriya.

Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan.
Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan. REUTERS/IntelCenter/Handout
Talla

Wata sanarwa da shugaban kungiyar, Abubakar Shekau, ya aikawa manema labarai yace, kungiyar ba zata koma teburin tattaunawa ba, kuma nan bada dade wa ba zasu rusa Gwamnatin Tarayya tare da kafa shari’ar Musulunci.

Kungiyar ta bukaci kafofin yada labarai yada martaninsu, kamar yadda aka yada kalaman Sheikh Dahiru, ko su dauki matakin kai wa kafafen yada labarai hari.

Kungiyar ta dauki alhakin kashe mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan, Sale Abubakar Ningi, da kuma alkawarin ci gaba da kai hare hare ga fitattun mutane.

Sakon kungiyar ta karkashin Abul Qaqa sun yi kira ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kare mutuncinsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.