Isa ga babban shafi
Afrika

Sharhin wasu Jaridun Afrika

Labarin yunkurin kisan Fira ministan kasar Kenya Raila Odinga da tasirin siyasar Turai da maganar wasannin kwallon kafa na zuwa Olympics a London sune wasu daga cikin labaran da suka mamaye jaridun Afrika.

Jaridun Afrika a cikin Taswirar Afrika
Jaridun Afrika a cikin Taswirar Afrika
Talla

Jaridar Standard ta kasar Kenya ta ruwaito wani babban Jami’in gwamnatin kasar Jakoyo Midiwo, yana shaidawa ‘Yan Sanda cewa cikin Ministocin Odinga da wasu manyan Jami’an tsaro sun shirya minakisar yadda zasu kashe Fira minista Raila Odinga.

Sai dai Jaridar tace gwamnatin kasar ta lura bubu shaida da zai tabbatar da labarin zargin da Mista Midiwo ya ke yi.

Sai dai Mista Midiwo yace ya fahimci haka ne ta karkashin wani amininsa da ba zai iya fallasa sunansa ba.

Yanzu haka Jaridar The Standard tace akwai Sammace da ke jiran Midiwo idan ya tako da kafar shi cikin Kenya daga Afrika ta Kudu.

A cewar Jaridar Mataimakin Fira Minista Uhuru Kenyatta da ministan Kudin Kenya Njeru Githae da Sam Ongeri suna cikin wadanda Midiwo yace suna kokarin kisan Odinga.

Labarin makomar tattalin arzikin Turai shi ne ya mamaye wasu jaridun hada hadar kudade a kasar Afrika ta Kudu.

Babban Labarin Jaridar Business Daily, Shi ne “ Matsalar Tattalin arzikin Turai hannayen jari sun shiga tsaka mai wuya”

Jaridun sun yi bayani game da fargabar da ‘yan kasuwa suka nuna sanadiyar rikicin kasar Holland da ya janyo gwamnatin kasar yin murabus.

Akwai kuma fargaba game da yiyuwar faduwar Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a zaben shugaban kasa wanda yana cikin shugabanni masu fadi tashi wajen daidaita matsalar tattalin arzikin Turai.

Yawancin Jaridun Afrika a shafinsu na wasanni sun dauki labarin samun hurumin shiga wasannin kwallon  kafa na Olympics da kasar Senegal ta samu bayan ta doke Oman ci 2-1 a birnin Coventry.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.