Isa ga babban shafi
Senegal

Abdoulaye Wade ya amsa shan kaye a zaben Senegal

Shugaba Abdoulaye Wade, ya amsa shan kaye a zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka gudanar a kasar Senegal, inda abokin takararsa Macky Sall, ya samu rinjayen kuri’u, nasarar da ta kawo karshen yunkurin Tazarzen Wade akan madafan iko.

Tsohon shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade da Zababben shugaban kasa Macky Sall
Tsohon shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade da Zababben shugaban kasa Macky Sall Photo : Reuters/Montage : RFI
Talla

Dubban mutane ne suka hada gangami a birnin Dakar, don bikin murnar nasarar Macky Sall,  wanda ya kawo karshen yunkurin tazarcen Shugaba Wade, mai shekaru 85 na haihuwa, da ya kwashe shekaru 12 bisa karagar mulki.

Rehotanni daga Senegal na bayyana cewa Wade ya kira abokin hamayyar shi Macky Sall ta wayar Salula a dai dai karfe 9:00 na yamma a jiya Lahadi domin taya shi murnar lashe zabe.

Mutane da dama dai sun yi hasashen ballewar rikici idan har Wade ya cim ma nasarar yin Tazarce. Sai dai kayen da shugaban ya sha yasa hankalin duniya ya kwanta saboda ci gaban demokradiya a cikin kasar.

Tun lokacin da Wade ya bayyana kudirin yin tazarce wa’adi na uku zanga zanga ta barke a kasar Senegal al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6 kafin gudanar da zaben zagaye na farko a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Tuni dai shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya yi jinjina ga kasar Senegal game da sakamakon zaben da ya ba Macky Salla nasara inda tun a farko kasar Faransa da Amurka suka bukaci Wade yin murabus daga kudirin shi na Tazarce.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.