Isa ga babban shafi
Mali

Sojoji sun kifar da gwamnatin Mali

Sojoji da ke bore a kasar Mali, sun sanar da kifar da gwamnatin Amadou Toumani Toure, da Ministocinsa tare da dakatar da kundin tsarin mulkin kasar da karbe ikon kafafen yada labarai, bayan kwashe yammacin jiya ana musayar Albarussai.

Sojojin kasar Mali a Bamako babban birnin kasar Mali
Sojojin kasar Mali a Bamako babban birnin kasar Mali AFP PHOTO / HABIBOU KOUYATE
Talla

Sojojin wadanda suka ayyana kansu a matsayin masu kokarin girka Demokradiyya sun ce sun karbe ikon gwamnati ne saboda gazawar gwamnatin Amadou Toumani Toure wajen yaki da ‘Yan Tawayen abzinawa.

Wani kakakin Sojin Amadou Konare ya shaidawa kamfanin Dillacin Labaran Faransa AFP cewa sun karbe madafan ikon Mali ne saboda halin da kasar ta shiga da gazawar Gwamnati wajen yaki da ta’addanci.

Sai dai Mista Konare yace zasu mika mulki ga farar hula bada jimawa ba.
Jagoran kifar da gwamnatin Mali Kaftin Amadou Sanogo ya fito a kafar Telibijin inda yake bayyana dokar hana fita a kasar.

Yanzu haka dai rehotanni daga Fadar shugaban kasa na nuni da cewa shugaba Amadou Toumani ya fice daga fadar gwamnatin kasar.

Tun bayan samun labarin musayar Albarussai a fadar shugaban kasa, Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Faransa da Amurka suka bukaci kai zuciya nesa.

Wannan Juyin mulkin na zuwa ne bayan Shugaba Toure ya bayyana matakin sauka daga mukamin shugaban kasa a zaben watan Afrilu da za’a gudanar bayan yin wa’adi biyu saman mulki.

Hambararren shugaban kasa Amadou Toumani Toure, tsohon Soja ne wanda ya jagoranci juyin mulkin da aka yi wa moussa Traore a shekarar 1991 kafin mika mulkin ga farar hula. A shekarar 2002 ne aka zabi Toure matsayin shugaban kasa tare da sake zaben shi a shekarar 2007.

A zamanin mulkin Toure ana yabon shi wajen yunkurin tunkarar ‘yan Tawayen Tuareg wadanda suke yaki da gwamnatin Mali tun samun ‘Yancin kai.

Sai dai a bayan bayan nan rikicin ‘Yan tawayen ya sa mutane sama da 200,000 yin kaura daga kasar Mali.

An bayyana cewa mutane sama da Miliyan 1.5 ne suka yi kaura zuwa kasashen Aljeriya da Burkina Faso da Libya da Nijar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.