Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Wani Rehoton MDD ya zargi dakarun Congo da kashe mutane 33

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya zargi sojoji masu biyayya ga shugaba Kabila na Jamhuriya Demokradiyar Congo da alhakin kashe akalla mutane 33 a Kinshasa babban birnin kasar, a lokacin da aka aiwatar da zaben shugaban kasa, a bara.

Wasu 'Yan Congo dauke da gawar wani mutum wanda dakarun sojin congo suka kashe
Wasu 'Yan Congo dauke da gawar wani mutum wanda dakarun sojin congo suka kashe Reuters
Talla

Rahoton na Hukumar gamayyar masu sa ido lura da hakkin bil’adama ya nuna cewa soji masu biyayya ga shugaba kabila sun kashe akalla mutane 22 kafin zabe, mutane kuma 16 ne suka bace ba tare da jin duriyar su ba bayan zabe.

Kamfanin Dillanci labaran Reuters ya bayyana cewa rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna yadda dakarun kasar Congo suka nuna ba sani ba sabo kan abokan hamayya da gwannati ta hanyar yankasu da dirka masu allura da wani sinadari da ba a tantance shi ba.

An bayyana kuma sojajin suna jefa gawawwakin mutane a cikin kogin Congo da ke kusa da fadar kabila bayan kashe su.

Zaben wanda aka gudanar a watan Nuwamba an bayyana cewa Mista Kabila ne ya lashe inda ‘yan hamayya suka yi watsi da sakamakon zaben.

Tuni Ministan shari’ar kasar Mista Luzolo Bambi lessa ya yi watsi da rahoton wadda ya ce akwai siyasa a cikinsa, don a cewarsa bisa binciken ‘Yan sandan kasar mutane 20 suka hallaka a hanun abokan hammayya na jam’iyar dan takara Etienne Tshisekedi wadda a halin yanzu ke karkashi daurin talala bayan ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.