Isa ga babban shafi
Libya-Mauritanie

Mahukumtan kasar Mauritaniya sun cebke Abdallah Alsanusi na Libya

Mahukumtan kasar Mauritaniya sun bayyana cebke tsohon shugaban hukumar Leken Asirin tsohon shugaban kasar Libiya Ma’amar Kadhafi, cewa da Abdallah al-SanoussiAlsanusi da ke boye tun bayan faduwar gwamnatin Kadhafi, an kama shi ne a daren jiya juma’a a filin saukar jiragen saman Nouakchott na kasar Mauritaniya.al-Sanussi daya daga cikin mutanen da kotun duniya ke nema ruwa jallo, ya fada hannu ne, bayan da ya biyo wani jirgin saman fasinja, daga birnin Casablanca na kasar Maroko.Tuni dai gwamnatin kasar faransa ta bayyana cewa, zata nemi mahukumtan kasar Mauritaniya da su gaggauta iza keyar al-Sanusi zuwa kotun duniya.  

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.