Isa ga babban shafi
Libya

Jalil ya yi jawabin farko a Tripoli

Shugaban gwamnatin rikon kwarya a kasar Libya Mustafa Abdel Jalil, ya yi gargadin kaucewa daukar fansa lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa na farko a Tripoli, bayan wasu jerin hare hare da masu biyayya ga Gaddafi suka kaddamar.A wani mataki na kawo cikas ga sabuwar gwamnatin rikon kwarya, dakarun Gaddafi sun kashe mutane 15 a wani samame da suka kai a matatar man Fetir din kasar.Duk da wadannan hare hare shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mustafa Abdel Jalil ya samu kwarin gwiwar gabatar da jawabinsa a gaban dubun dubatar mutane.Sai dai kuma a wani sako da Shugaba Gaddafi ya aika wa wata kafar Telebijin din kasar Syria, shugaban yace har yanzu yana cikin Libya tare da jaddada cewa ba zasu sake hannunta kasar Libya ba ga turawan mulkin mallaka. 

Mustafa Abdel Jalil, Shugaban 'Yan Tawayen Libya
Mustafa Abdel Jalil, Shugaban 'Yan Tawayen Libya REUTERS/Esam Al-Fetori
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.