Isa ga babban shafi
Tunisiya

Ana zaman makoki na kwanaki 3 a Tunisiya

A yau Juma’a Gwamnatin kasar Tunisiya ta ware kwanaki uku ga al’ummar kasar don juyayin dabun dubatar al’ummar kasar da aka kashe sanadiyar zanga zangar da ta yi sanadiyar hambarar da gwamnatin Shugaba Zine al-Abidine Ben Ali.A wani bayani da gwamnatin kasar ta sanar bayan kammala taron majalisar ministoci a jiya alhamis, sanarwar tace makarantun Sakandare da Jami’o’in kasar da tuni aka rufe su zasu dawo aiki a ranar litinin ta makon gobe.Lokacin da ya ke ganawa da manema labarai bayan kammala taron ministocin, Mohamed Aloulou, ministan kula da wasannin kasar yace harakokin wasannin da suka tsaya cak makwannin biyu da suka gabata, yace nan bada jimawa bane zasu ci gaba.Akalla mutane 78 ne suka mutu tun bayan fara rikicin kasar, kuma rikicin ya yi sanadiyar hasarar kudade sama da biliyan 3 na Dinar a kasar, kamar yadda Ministan cikin gidan kasar Ahmad Friaa ya sanar. 

wani dan kasar Tunisiya rike da tuta lokacin rikicin kasar
wani dan kasar Tunisiya rike da tuta lokacin rikicin kasar Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.