Isa ga babban shafi
Tunisiya

Za’a hukunta wadanda suka haddasa rikicin Tunisiya

Sabuwar gwamnatin Prime Ministan Tunisiya Mohammed Ghannouchi ta bayyana kudirin hukunta duk wadanda ta kama da haddasa boren da ya hambarar da shugaban kasar Zine El Abidine Ben Ali. A wata hira da shugaban ya yi da kafar rediyon Faransa dake yada labaran Nahiyar Turai, shugaban ya wanke ministocin da suka yi aiki karkashin gwamnatin Ben ali wadanda ya bayyana masu kishin kasa.A jiya litinin ne dai aka samar da sabuwar gwamnatin hadin gwiwa a kasar inda shugabannin jam’iyun adawar kasar guda uku suka samu kansu a cikin sabuwar gwamnatin rikon kwarya, kwanaki uku bayan faduwar mulkin kama karyar tsohon shugaban kasar Ben Ali, sakamakon juyin juya halin da matasa suka assasa saboda matsalar rashin aiki a kasar.Sai dai kuma Mista Ghannouchi yace zai hukunta duk jam’ian tsaron da gwamnatinsa ta kama da kurara rikicin kasar. A cewarsa babu wanda suka baiwa umurnin buda wuta don daukar mataki ga zangar zangar.A yanzu haka dai Jam’iyyar RCD ta hambararren shugaban kasar ita ke rike da kujerun ministan Cikin gida da na kasashen waje da ministan tsaron kasar, duk da boren da ‘yan kasar suka gudanar na ganin kawo karshen mulkin jam’iyyar a kasar. 

Prime Minister kasar Tunisiya Mohamed Ghannouchi
Prime Minister kasar Tunisiya Mohamed Ghannouchi Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.