Isa ga babban shafi
Tunisiya

Hukumomin kasar Tunisiya Sun Tura Soja Muhimman Wurare

Hukumomin kasar Tunisiya sun tura Sojan  kasar sassa birnin Tunis domin taimakawa maido da Doka da Oda, yankunan da jama'a ke cigaba da bore  saboda rashin ayyukan yi da matsalar halin rayuwa.Wasu bayanai na cewa mutane akalla 50 ne suka gamu da ajalin su sakamakon wannan  bore dan tsakanin nan.Motojin Soja na yaki sunyi ta sintiri titunan Tunis tun wayewar gari yau.An kuma tura Dakaru zuwa yammacin babban birnin kasar inda boren yafi kamari.Jiya masu bore sunyi ta jifan ‘Yan Sanda da duwatsu a yankin Ettadamen, inda aka kona motoci da damaWannan shine karo na farko da Hukumomin kasar suka tura sojoji domin kwantar da kura tun da aka fara wannan bore. 

Wata motar Soja dake sintiri a  Ettadhamen kusa da  Tunis
Wata motar Soja dake sintiri a Ettadhamen kusa da Tunis rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.